Isa ga babban shafi

Najeriya ta tafka asarar dala biliyan 9 a ibtila'in ambaliyar bara -NBS

Hukumar kididdiga ta Najeriya ta ce jumullar asarar da kasar ta tafka sakamakon ibtila’in ambaliyar ruwan da ta faru a bara ya kai dala biliyan 9 da miliyan 100 da 20.

Wani yanki da ambaliya ta yiwa illa.
Wani yanki da ambaliya ta yiwa illa. © Reuters
Talla

Shugaban sashen tattara alkaluma na hukumar kididdiga ta Najeriyar Adeyemi Adeniran a jawabin da ya gabatar yayin kaddamar da rahoto kan shirin farfado da sassan da ambaliyar ta yiwa illa da ya gudana a ofishin Majalisar Dinkin Duniya da ke Abuja, ya ce gwamnatin Najeriyar da hadin gwiwar Bankin Duniya sun yi kiyasin ambaliyar da aka tafka ta iya haura dala biliyan 3 da miliyan dari 7 da 90 amma bayan sake nazartar ibtla’in alkaluman suka tsaya akan yiwuwar asarar ta kai dala biliyan 9 da miliyan dari 1 da 29.

A cewar babban jami’in zuwa ranar 25 ga watan Nuwamban shekarar 2022 jumullar asarar da Najeriyar ta tafka ya tsaya a dala biliyan 6 da miliyan 600 da 80 ba tare da tattara alkaluman munanan ambaliyar da aka gani daga bayan wancan lokacin ba.

Jihohi da dama ne suka tafka asara a mummunar ambaliyar ta shekarar 2022 wadda ta yi matukar muni a tarihi da ta shafi kaso mai yawa na amfani gonar da aka yi a shekarar.

A jihar Anambra alkaluma sun nuna yadda kashi 99.1 na amfani gona ya bi ambaliyar sai Kogi da kashi 99.7 kana Jigawa da kashi 97.1 baya ga wasu kain jihohi 6 da ambaliyar ta shafa, ibtila’in da masana ke kallo a matsayin musabbabin karancin abinci a sassan Najeriya.

A bangaren rushe tarin gidaje kuwa , hukumar gididdigar ta Najeriya ta ce Bayelsa ce kan gaba kana Jigawa sai jihar Nasarawa a Kogi da kuma Delta sannan Anambra.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.