Isa ga babban shafi

Watanni hudu bayan harin soji a Tudun-Biri har yanzu an gaza biyan jama’a diyya

Yau Laraba 3 ga watan Afrilu ake cika watanni 4 cur da kuskuren harin da sojoji suka kai garin Tudun Biri na Karamar Hukumar Igabi a jihar Kaduna ta arewacin Najeriya, sai dai har zuwa yanzu gwamnati ba ta biya diyyar ko da mutum guda cikin dimbin mutanen da harin ya kashe ba.

Mataimakin shugaban Najeriya Kashim Shettima a lokacin da ya ziyarci mutanen da ke jinya a asibiti sakamakon harin bam da ya rutsa da su a Tudun-Biri a jihar Kaduna.
Mataimakin shugaban Najeriya Kashim Shettima a lokacin da ya ziyarci mutanen da ke jinya a asibiti sakamakon harin bam da ya rutsa da su a Tudun-Biri a jihar Kaduna. © aminya
Talla

A ranar 3 ga watan Disamban bara ne, wani hari da sojojin Najeriya suka kai da jirage marasa matuki ya kashe tarin mutanen da ke tsaka da taron mauludi a garin na Tudun Biri lamarin da ya tayar da hankalin al’ummar kasar.

Tun a kwanaki kalilan bayan faruwar harin ne gwamnatin Najeriya karkashin jagorancin shugaba Bola Ahmed Tinubu ta sha alwashin biyan diyyar daukacin mutanen da harin sojojin ya kashe da yawansu ya haura 120 baya ga sake gina kauyen baki daya.

RFI Hausa ya ziyarci Tudun-Biri don ganin halin da ake ciki

A ziyarar gani da ido da sashen Hausa na RFI ya kai garin na Tudun Biri wakilinmu ya iske yadda gwamnatin jihar Kaduna ta faro ginin Masallachi wanda aka yi a daidai wajen da harin ya kashe taron 'yan mauludin, sai kuma titin da ke shiga garin da shi ma aka faro aikinsa baya ga rijiyar burtsatse, sai dai babu batun biyan diyya da kuma sake gina garin daga bangare gwamnatin Tarayya.

Haka zalika har zuwa yanzu al’ummar garin ba su iya samun kudaden da wasu daidaikun jama’a suka tallafa musu da shi ba, kodayake dai an umarce su da su bude asusun ajiya na banki don sanya musu kudaden.

Kungiyar Gwamnonin Arewacin Najeriyar sun bai wa mutanen Tudun-Biri tallafin naira miliyan 180.
Kungiyar Gwamnonin Arewacin Najeriyar sun bai wa mutanen Tudun-Biri tallafin naira miliyan 180. © Gombe state government

RFI ya gano cewa kawo yanzu an sallami ilahirin mutanen da suka jikkata a harin sojojin na ranar 3 watan Disamba, duk da cewa har yanzu suna ziyartar asibiti don duba wasu raunuka da suka samu lokaci zuwa lokaci.

Dangane da batun gidaje RFI ya gano cewa har zuwa yanzu ba a cika alkawarin gidaje da gwamnatin Najeriyar ta daukar wa al’ummar garin na Tudun Biri ba.

Babu abin da aka ba ni na diyya

Malam Auwal Shehu wanda ya rasa yaronsa guda sai kuma yarinyarsa daya da ta jikkata ya ce har zuwa yanzu bai samu diyyar ba, sai dai zaman jiran tsammani, yayin da Jafar Abdullahi wani mazaunin garin ke cewa iyakar kudaden da al’ummar garin suka samu kawo yanzu shi ne tallafin dubiya da masu ziyara ke bai wa marasa lafiya a asibiti.

Sai dai Muhammad Dahiru Bello Buruk guda cikin jagororin kwamitin da aka kafa don aikin tattarawa da kuma rarraba kudin, ya ce zuwa yanzu ba su da alkaluman kudaden da aka tara da yawansu ya haura miliyan 130 kuma suna fatan wani lokaci a nan gaba a rarrabawa jama’a wannan tallafi.

Gen Lagbaja with members of Kaduna community
Gen Lagbaja with members of Kaduna community © Nigerian Army

A ranar 26 ga watan Maris din da ya gabata ne gwamnatin jihar Kaduna karkashin jagorancin Uba Sani ta aza harsashin ayyukan ginin masallachi da titi baya ga rijiyoyin burtsatse a garin na Tudun Biri wanda ke matsayin wani bangare na alkawuran da gwamnan ya dauka tun a lokacin  faruwar lamarin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.