Isa ga babban shafi

Tinubu ya bada umarnin sake gina kauyen Tudun Biri dake Kaduna

Najeriya – Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bada umarnin sake gina garin Tudun Biri baki daya domin samar da ingantattun gidaje ga daukacin mazauna kauyen, sakamakon iftila'in da ya afka musu wanda yayi sanadiyar rasa dimbin rayuka.

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu © Bola Ahmed Tinubu twitter
Talla

Gwamnan Jihar Kaduna Sanata Uba Sani ya bayyana haka lokacin da ya ziyarci kauyen tare da mai baiwa shugaban kasar shawara a kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu domin sake jajanta musu da kuma gabatar musu da wannan albishir.

Sanata Sani yace ana shirya yadda za'a tantance wadanda hadarin ya ritsa da su domin biyansu diyya, yayin da aka sanya malaman addini a ciki domin ganin anyi abinda shari'a ta tanada.

Shugaban rundunar sojin Najeriya Janar Taoreed Lagbaja lokacin da ya ziyarci kauyen Tudun Biri
Shugaban rundunar sojin Najeriya Janar Taoreed Lagbaja lokacin da ya ziyarci kauyen Tudun Biri © Premiumtimes

Gwamnan yace bayan biyan diyyar, za'a gina gidaje ga daukacin mazauna kauyen tare da asibiti a karkashin wani sabon tsari na wannan gwamnati domin ganin jama'ar Tudun Biri sun amfana.

Sanata Sani yace dama an shirya irin wannan aiki ne a jihohi 7, amma yanzu shugaban kasa ya bada umarnin cewar a fara da Tudun Biri kafin kaiwa zuwa sauran jihohin da aka tsara.

Sanata Sani yace suna fatar ganin aikin ya kankama nan da makonni biyu masu zuwa, yayin da ya tabbatar da cewar za'a yiwa mutanen wannan kauye adalci.

Gwamnan jihar Kaduna Sen. Uba Sani yayin bukin kaddamar da horon sabbin 'yan banga a jihar. 02/09/23
Gwamnan jihar Kaduna Sen. Uba Sani yayin bukin kaddamar da horon sabbin 'yan banga a jihar. 02/09/23 © Sen. Uba Sani X handle

A nashi jawabi, Malam Nuhu Ribadu wanda ya yabawa malaman addini a kan rawar da suke takawa na kwantar da hankalin jama'a da kuma kiran biyan su hakkin da ya rataya a kan gwamnati, yace shugaba Tinubu ya kadu da lamarin, abinda ya sa kowacce sa'a sai ya tambayi halin da wadanda hadarin ya ritsa da su ke ciki.

Mai baiwa shugaban shawara yace suna iya kokarinsu a gwamnatance wajen ganin an tabbatar da tsaro ga jama'a baki daya saboda sun san cewa Allah zai tamabaye su a kai.

Daga cikin wadanda suka ziyarci kauyen ayau harda manyan kwamandodin sojin kasa da sama, da jami'an tsaro daga bangarori da dama da Sanata Shehu Buba dake jagorancin kwamitin tsaro a majalisar dattawa da kuma Sheikh Musa Assadus Sunnah.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.