'Yan Najeriya na ci gaba da cece-kuce kan kisan masu Maulidi a Kaduna
Wallafawa ranar:
Kunna - 15:00
Hukumar bada agajin gaggawa ta Najeriya reshen shiyar Arewa maso yamma, ta ce mutane 85 ne suka rasa ransu a harin bom din da sojoji suka kai, sannan akwai wasu 66 da ke samun kulawa a asibiti.
Mafi yawan wadanda lamarin ya shafa dai mata ne da kananan yara da kuma dattijai a lokacin da suke gudanar da Mauludi, a kauyen Tudun Biri da ke karamar hukumar Igabi da ke Jahar Kaduna.
'Yan Najeriya na ci gaba da cece-kuce kan wannan ibtila'i da ba wannan ne karon farko da yake faruwa akan fararen hula ba.
Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu