Isa ga babban shafi

Najeriya:'Yan bindiga sun sake sace mutane 87 a sabon harin da suka kai Kaduna

‘Yan bindiga sun sake yin awon gaba da mutane 87 a cikin daren Lahadi, bayan da suka kai wani sabon hari a kan kauyen Kajuru Station da ke karamar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna a Najeriya.

Wannan harin na zuwa ne kwanaki biyu bayan sace wasu mata 15 a Kajuru.
Wannan harin na zuwa ne kwanaki biyu bayan sace wasu mata 15 a Kajuru. REUTERS/Goran Tomasevic/File Photo
Talla

Wani matashi daga kauyen Kajuru station, Harisu Dari, ya tabbata da aukuwar lamarin a wannan Litinin, inda ya ce ‘yan ta’adan sun fasa shaguna sun kwashi  kayan dimbim abinci, kamar yadda jaridar ‘Punch’ da ake wallafawa a kasar ta ruwaito.

Wannan harin na zuwa ne kwanaki biyu kacal bayan da aka sace wasu mata 15 da wani mutum guda a kauyen Dogon-Noma da ke karamar hukumar.

A cikin makwanni biyu da suka wuce, kananan hukumomin Kajuru da Chikun sun kasance wuraren da aka yi ta sace mutane, lamarin da ya tada hankalin al’ummar jihar.

Rahotanni sun ce ya zuwa safiyar Litinin din nan, babu jami’an tsaro da aka gani a wannan kauyen, lamarin da ya jefa al’ummar yankin cikin rudani.

Babu wani bayani daga rundunar ‘yan sandan jihar ya zuwa lokacin hada wanan rahoto, kuma duk kokarin da aka yi na tuntubar jami’in yada labarai na rundunar, ASP Mansir Hassan ya ci tura.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.