Isa ga babban shafi

'Yan bindiga sun sake garkuwa da mutane 61 a jihar Kaduna

‘Yan bindiga sun kai farmaki a garin Buda da ke karamar hukuma Kajuru a Jihar Kadunan Najeriya inda suka yi garkuwa da akalla mutane 61.

'Yan bindiga sun addabi wasu yankuna a jihohin Najeriya.
'Yan bindiga sun addabi wasu yankuna a jihohin Najeriya. © Leadership
Talla

A cewar wani shaidan gani da ido Dauda Kajuru, ‘yan ta’addan da suka shiga cikin kauyen suna da yawa sosai yayin da suka dinga Harbin iska suna, inda ya ce sun zo da niyar sace mutanen da suka fi na daliban Chikun, amma zuwan sojoji ya saka lamarin yin sauki.

Ya kara da cewa a cikin jama’ar da aka yi garkuwa da su akwai ‘yan uwansa, sannan a labarin da su ke samu a lokacin shi ne har yanzu ‘yan bindigar da mutanen ba su karasa wurin da za su je ba.

Wani mazaunin garin da akwai matarsa cikin wadanda aka yi awun gaba da su, ya ce a cikin mutune 61 akwai mata, da yara da kuma masu shayarwa.

Wannan dai na zuwa ne a kasa da sati da ‘yan ta’adda suka sace mutane sama 287 a garin Kuriga ciki har da dalibai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.