Isa ga babban shafi

'Yan bindiga sun sake kai hari Kajuru tare da sace mata 7

‘Yan bindiga sun sake kai wani sabon hari garin Banono da ke karkashin masarautar Kufana ta karamar hukumar Kajuru da ke Jahar Kaduna a tarayyar Najeriya, inda suka kashe mutum daya da kuma yin garkuwa da wasu mutane 8.

Gwamnan jihar Kaduna Sen. Uba Sani.
Gwamnan jihar Kaduna Sen. Uba Sani. © Sen. Uba Sani X handle
Talla

Jaridar Daily Trust da ake wallafawa a kasar ta bayyana cewar, ‘yan bindigar sun kashe Christopher Zamani da raunata wata mata Mary Isah wacce ke kwance a wani asibiti da ke Maraban Kajuru.

Haka nan jaridar ta ce ‘yan bindigar sun kuma yi garkuwa da wasu matan da suka hada da Tina Bulus da Alice Joshua da Sarah Micah da Jenet Amos da Martha Peter da Rita Geoffrey da Favour Ado sai kuma namiji daya Kaduna Fidelis.   

A wani labarin kuwa, mutane 24 daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su a garin Buda a ranar Litinin din da ta gabata duk a karamar hukumar ta Kajuru, sun kubuto daga hannun wadanda suka yi garkuwa dasu.

Wani mazaunin garin Benjamin Yuhana, ya ce mutanen sun dawo gida ne ba tare da an biya ko sisin kobo ba a matsayin kudin fansa, duk da cewa haryanzu akwai wasu da dama a hannun masu garkuwa da mutanen.

A baya-bayan nan dai, jahar Kaduna ta na fuskantar kalubalen tsaro da garkuwa da mutane, daga cikin akwai na sace dalibai 287 da ‘yan bindiga suka yi a garin Kuriga da ke karamar hukumar Chikun.

A lokacin wata zantawa da aka yi da Kwamishiniyar Kula da Jin dadi da Walwalar Al’ummar Jihar Kaduna Hajiya Rabi Salisu, ta ce gwamnatin Jahar na aiki tukuru don ganin an kubutar da daliban.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.