Isa ga babban shafi

Gwamnatin Najeriya ta koka kan karuwar adadin yaran da ba sa zuwa makaranta

Ministan ilimin Najeriya Yusuf Sunusi, ya ce adadin yaran da basa zuwa makaranta a kasar ya kai wani hali da ke matukar tayar da hankali.

Wasu kananan yara 'yan makaranta. (Hoto domin misali)
Wasu kananan yara 'yan makaranta. (Hoto domin misali) © UNICEF
Talla

Rahoton da ministan ya bayyana, ya nuna cewar Jihar Kaduna da ke arewacin kasar, na da yara dubu 680 da suka daina zuwa makarantu, duk kuwa da yunkurin da gwamnatin da ta gabata a jihar tayi na magance matsalar.

Sabbin alkaluman da gwamnatin Najeriyar ta fitar dai sun karuwar yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a jihar ta Kaduna, idan aka kwatanta da adadin yara dubu 500 da gwamnan Jihar Uba Sani ya bayyana a watan Satumban shekarar nan ta 2023.

Daga jihar ta Kaduna, wakilinmu Aminu  Sani Sado ya yi nazari kan matsalar tare da aiko mana da  traho, wanda za a iya saurara idaan aka latsa alamar sautin da ke sama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.