Isa ga babban shafi
Najeriya

Sojan Najeriya sun kashe 'yan Boko Haram da dama a Konduga

Rundunar sojan Najeriya ta sanar da Kashe 'ya 'yan kungiyar Boko Haram kusan 100, a garin Konduga dake jihar Borno a arewacin kasar.Kakakin runduna ta 7 ta sojan dake Maiduguri, Kanar Sani Usman ya shaida wa Radiyon Faransa cewa, an kashe mayakan na Boko Haram ne, a wani artabun da suka yi da dakarun kasar.Sojojin sun bayar da sanarwar kwace motoci dake dauke da makaman harba roka da bindigogi da kuma harsasai da dama, wadanda yanzu haka aka kaisu birnin Maiduguri.Wannan artabu na zuwa ne kwana daya, bayan da dattawan jihar ta Borno sun yi korafi kan cewa 'yan kungiyar ta Boko Haram sun yi wa birnin Maiduguri kawanya, kuma zasu iya farwa garin a kowane lokaci.

Wasu sojojin Najeriya a kusa da dajin Sambisa
Wasu sojojin Najeriya a kusa da dajin Sambisa Ben Shemang / RFI
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.