Isa ga babban shafi
Najeriya-Kamaru

An daure 'yan Boko Haram 14 a Kamaru

Wata kotun soja a kasar Kamru ta yanke wa ‘yan kungiyar Boko Haram 14 hukuncin daurin daya kai tsawon shekaru 20 a gidan yari. A watan Maris da ya gabata aka kama mutane, bayan da aka same su da muggan makai, kuma suka amince da cewa su ‘yan kungiyar ta Boko Haram ne a Nigeria.Mutane sun amsa laifin ne yayin wani zaman jin bahasi, da aka yi a birnin Maroua dake arewacin kasar.Kotun ta same su laifukan da suka hada da mallakar makamai ba bisa ka’ida ba, da kuma yunkurin tayar da zaune tsaye, don haka ta yanke musu hukuncin daya kama daga shekaru 10 zuwa 20 a gidan yari. 

Wasu  'yan kungiyar Boko Haram a Najeriya
Wasu 'yan kungiyar Boko Haram a Najeriya
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.