Isa ga babban shafi
Najeriya-Kamaru

An binne Sojojin Kamaru da suka mutu a yakin Boko Haram

An yi bukin binne gawarwakin sojojin kamaru 26, da suka rasa ransu yayin fafatawa da ‘yan kungiyar Boko Haram a lardin arewa mai nisa. Wakilin mu a yankin Ahmed Abba yace dubun dubatar ‘yan kasar ne suka taru a Karte Janaral, dake Yaounde Babban birnin kasar, domin halartan bukin girmama Sojojin.Bukin ya gudana ne a gaban ministan tsaron kasar Alain Edgar Mebe Ngo'o.Anyi wa Sojojin faretin bangirma wanda daya daga cikin abokin aikinsu ya jagoranta, bayan da aka likawa gawakin Lambar yabo, Kuma shugaba Paul biya tace su bayar da ransu don ceto kasarsu. 

Gawarwakin Sojan Kamaru, lokacin da ake musu janaiza
Gawarwakin Sojan Kamaru, lokacin da ake musu janaiza
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.