Isa ga babban shafi
MDD

Ban ki-Moon ya bukaci a mayar da hankali wajen kawar da fatara a duniya

Babban Sakataren Majalisar dinkin duniya Ban Ki-moon ya nemi kasashen duniya da su Jingine duk wani son zuciya a fuskanci matakan kawar da fatara da jama’a ke fama dashi.

Sakatare Janar na MDD Ban ki-Moon ya yin jawabinsa a dakin taro na Habasha
Sakatare Janar na MDD Ban ki-Moon ya yin jawabinsa a dakin taro na Habasha REUTERS/Tiksa Negeri
Talla

Kallaman Ban ki-moon na zuwa ne, yayin jawabi sa  a taron kwana biyu da aka bude a Habasha a game da shata sahihiyar hanyar fita daga kangin fatara a duniya a kokarin cim ma muradan karni.

Taron da ake yi a Habasha ya kasance na uku, bayan da aka gudanar da irin wannan taro a Monterrey cikin shekara ta 2002 da wanda akayi a Doha cikin shekarar 2008.

Muhimman batutuwa da taron ya mayar da hankali shi ne  shata matakan bunkasa kasashe masu tasowa, dake fuskantar gibin dala Trilliyan 2.5 duk shekara, a cewar kwaminitin  ciniki da raya kasa na majalisar.

Duk wannan ana ganin zai taimakawa Majalisar gabatar da tsarin cim ma muradan karni na shekara ta 2015 zuwa 2030, da ake sa ran zartarwa a New York cikin watan 10 mai zuwa.

Matakai 17 ne dai suka kunshi kawar da fatara a fadin duniya zuwa wadata jama'a da harkokin da suka shafi makamashi.

Sai dai kuma shata matsaya a game da taron da za ayi a New York na fuskantar matsala saboda yadda manyan kasashen duniya yawanci ke fama da matsalar kudi da sanyi-sanyi wajen tilastawa kamfanoni da masana'antu masu zaman kansu daukan wasu nauyi.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.