Isa ga babban shafi
Afrika ta Tsakiya

Ban Ki-moon ya nemi a tallafawa Sojoji a Afrika ta tsakiya

Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya yi kira ga kasashen Afrika su bayar da goyon bayansu da tallafin kudi zuwa ga dakarun da ke aikin wanzar da zaman lafiya a kasar Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya.

Sojan Afrika a kasar Jamhuriyyar Afrika ta Tsakiya a Bangui
Sojan Afrika a kasar Jamhuriyyar Afrika ta Tsakiya a Bangui REUTERS/Siegfried Modola
Talla

Mista Ban ya yaba da ikirarin sabuwar gwamnatin Bangui na samar da zaman lafiya a kasar bayan ya aika da sakon taya murna ga shugaba Catherine Samba Panza da Firaministanta Andre Nzapayeke.

Akwai kasashen Turai da suka amince su aika da dakaru zuwa Jamhuriyyar tsakiyar Afrika domin kwantar da rikicin kasar da ya lukume rayuka da dama tare da raba dubban mutane da gidajensu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.