Isa ga babban shafi
MDD-Africa

Ana Taron nazarin ci gaban kasashen Duniya a Habasha

Shugabanin kasashen duniya za su fara wani taro a yau Litinin a kasar Habasha kan yadda za a samar da kudaden gudanar da ayyukan ci gaba don kawo karshen yunwa da sauyin yanayi nan da shekara 2030 kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta tsara.

Thabo Mbeki, a Taron kasashen Afrika
Thabo Mbeki, a Taron kasashen Afrika Photo: South African government/Creative Commons License
Talla

Dalilin gudanar da wannan taron, wanda shi ne na uku bayan wanda aka yi a Monterrey a shekarar 2002 da Doha a shekarar 2008 shi ne tsara dokokin tabbatar da samun daidaito a duniya da kuma rage gurbatar muhalli.

Taron zai kuma mayar da hankali kan cike gibin zuba jari a fannoni da dama na ci gaba a kasashe masu tasowa wanda ake saran zai kai Dala tiriliyon biyu da rabi kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta tsara.

Wannan zai bai bai wa Majalisar damar gabatar da shirinta na ci gaba na shekarar 2015 zuwa 2030 wanda ake sa ran kaddamar da shi a watan Oktoba a birnin New York, da ya kunshi kawo karshen yunwa da kuma samar da wutar lantarki.

Masu shirya taron sun ce sun zabi Habasha ne saboda kasancewar ta a Afirka da ke dauke da kasashe 33 daga cikin 49 na duniya da ke fuskantar koma-baya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.