Isa ga babban shafi
China-Cuba

China ta ba Fidel Castro kyautar Nobel

China ta ba Tsohon Shugaban kasar Cuba Fidel Castro kyautar Nobel ta zaman lafiya. Jaridar da ke kusa da gwamnati tace Castro ya karbi kyautar ne saboda gudunmuwarsa ga samar da zaman lafiya a duniya.

Shugaban China Xi-Jinping tare da Fidel-Castro na Cuba
Shugaban China Xi-Jinping tare da Fidel-Castro na Cuba DR
Talla

Jaridar Global Times tace Fidel Castro ya lashe kyautar ne tsakanin ‘Yan takara 20 da suka hada da Shugabar Koriya ta Kudu Park Geun-Hye da Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon.

Kuma Jaridar tace Alkalai 9 da masana kusan 20 ne suka zabi Fidel Castro.

A 2010 ne China ta fara bayar da Kyautar, kuma Daliban Cuba ne a China suka karbi kyautar a madadin Castro.

Global Times tace masanan sun yi la’akari da yadda Castro ya kauracewa rikici ko amfani da karfi domin warware sabanin da ke tsakanin Cuba da wasu kasashe musamman Amurka.

Kuma Jaridar tace tun saukarsa daga mukamin shugaban kasa, Castro ke kokarin tattaunawa da shugabannin manyan kasashen duniya dangane da batun kawo karshen barazanar nukiliya a duniya.

Tsohon Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Kofi Annan ya taba lashe kyautar a 2012.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.