Isa ga babban shafi
Amurka

Obama na neman goyon bayan kasashen duniya don yakar IS

Shugaban Amurka Barack Obama wanda ke shirin gabatar da jawabi a gaban babban taron zauren MDD a cikin makon gobe, ya ce zai yi kokarin shawo kan kasashen duniya domin shiga rundunar da za ta yaki mayakan jihadi da ke kasar Iraki.

Shugaban Amurka, Barack Obama.
Shugaban Amurka, Barack Obama. REUTERS/Saul Loeb
Talla

Obama ya ce babbar manufar kafa rundunar shi ne gaggauta murkushe kungiyar ta IS wadda kawo yanzu ke ci gaba da yin tasiri a wasu yankuna na arewacin Iraki da kuma wani bangare na kasar Syria.

Kawo yanzu dai akwai kasashe akalla 10 da suka bayyana aniyarsu ta taimakawa domin fada da kungiyar wadda ta shelanta kafa daular musulunci a Iraki.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.