Isa ga babban shafi
Iraq-MDD

Sama da 'yan gudun hijira dubu 700 a arewacin Iraki

Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, ta ce kawo yanzu kimanin mutane dubu 700 ne suka gudu suka bar muhallansu, daga lokacin da mayakan da ke da’awar kafa Daular Islama suka soma kai hare-hare a yankin Kurdawa da ke kudancin Iraki.

'Yan gudun hijira a arewacin Iraki
'Yan gudun hijira a arewacin Iraki Reuters
Talla

Rahoton da ofishin hukumar da ke birnin Geneva ya fitar, ya bayyana cewa a halin yanzu akwai mutane sama da dubu 700 da suke tsere daga gidajensu kuma wannan matsala ta soma ta’azzara ne tun a cikin watan Yunin da ya gabata.

Adrian Edwards, shugaban hukumar ta UNHCR, ya ce a farkon wannan mako yawan kurdawan da sauran kabilun da suka bar muhallansu sakamokon hare-haren na mayakan da ke ikiran kafa daular Islama, sun kai dubu 600, to amma cikin kwanaki 4 da suka gabata an samu karin wasu ‘yan gudun hijirar akalla dubu dari daya a cewarsa.

Tuni dai hukumar ta soma aikin raba kayayyakin jinkai ga mazauna yankin na arewaci Iraki, inda take fatar raba akalla ton dubu 2 da 410 a cikin kwanaki 10, kuma za a raba wadannan kayayyaki ne ta hanyar yin amfani da jiragen sama da kuma motoci.

To sai dai Edwards ya ce babbar matsalar da ‘yan gudun hijirar suka fuskanta a yanzu ita ce rashin muhalli, domin da dama daga cikinsu na rayuwa ne a cikin wuraren ibada da kuma makarantu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.