Isa ga babban shafi
Iraq

An kashe 'yan Yazidi akalla 80 a arewacin Iraki

Hukumomin yankin Kurdistan mai cin gashin kansa daga kasar Iraki, sun ce mayakan Daular Islamiyya sun kashe ‘yan kabilar Yazidi akalla 80 a wani kauye da suka kai wa hari.

'Yan kabilar Yazidi a arewacin Iraki
'Yan kabilar Yazidi a arewacin Iraki REUTERS/Ari Jalal
Talla

Wani dan majalisar dokoki da ke wakilar yankin da lamarin ya faru Hoshiyar Zebari, ya bayyana cewa mayakan sun shiga garin ne inda suka tattara jama’a a wuri daya, inda suka kashe 80 daga cikinsu sannan suka awun gaba da wasu mata.

Yanzu haka dai MDD ta sanar da soma bincike domin tantance wadanda ke taimaka wa mayakan.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.