Isa ga babban shafi
Iraq

MDD za ta ladabtar da mayakan jahadin kasar Iraki

Majalisar Dinkin Duniya ta amince da kudiri ladabtarwa bisa yadda mayakann jahadi muslincin ke ci gaba da samun nasarar mamaye kasar Iraki

Mayakan sakai  yan Shi'a a Sadr City a Iraqi
Mayakan sakai yan Shi'a a Sadr City a Iraqi REUTERS/Stringer
Talla

Yanzu haka dai kasar Amruka na ci gaba da kai hare haren soja kan mayakan jahadin, da aka zarga da kai wani sabon hari kan yan kabilar Yazidi marasa rinjjaye dake yankin arewacin kasar

Daga karshen dai a nasa bangaren Farayi Ministan kasar Iraki Nuri Almaliki ya mika wuya , tare da amincewa ya sauka daga kan mukamin bisa matsin lambar kasashen duniya.

Har ila yau Nuri Almaliki ya yi fatan ganin sabuwar gwamnatin da za a kafa a kasar, zata iya kawo karshen ci gaba da samun nasarar da mayakan jahadi ke yi yanzu haka a kasar ta Iraki

A dai gefen kuma ministocin harakokin wajen Kungiyar Tarayyar Turai a jiya juma’a sun cimma matsaya wajen baiwa yan kabilar kurdawan kasar Iraki makamai domin kare kansu daga yaki da mujahidan dake son kafa kasar musulunci tsakanin kan iayakar kasashen Irak da Syriya suka kai masu
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.