Isa ga babban shafi
Iraq-MDD

Hukumar yan gudun Hijira ta MDD zata fara jefa kayyakin jinkai ta sama a kasar Iraki

Babban kwamishinan hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta MDD Andrian Edwards, ya sanar da cewa yanzu haka hukumar ta kaddamar da wani gagarumin shiri domin taimaka wa mutane rabin milyan a yankin arewacin kasar Iraki.

REUTERS/Rodi Said
Talla

Andrian wanda ke gabatar da jawabi a birnin Geneva, ya ce daga gobe laraba ne za su soma aikawa da kayayyakin jinkai ta sama, ta ruwa da kuma ta kasa zuwa yankunan da yakin da ake yi kasar ya shafa.

Hukumar ta bayyana cewa, nan da kwanaki 4 ne za a fara kaddamar da aikin jinkan inda jiragen saman zasu taso daga kasar Johdan da kuma Erbil babban birnin yankin Kurdistan mai cin kwarya kwayar cin gashin kai a kasar Iraki, sauran kwanaki 10 kuma hukumar yan gudun hijirar, zata aika kayayyakin jinkan ne, ta kasa daga wani ayarin motoci da zasu taso daga kasashen Turkiya da Johdan, daga karshe hukumar ta ce agajin zai biyo ta ruwa daga Dubai ta hanyar da ke ratsa kasar Iran.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.