Isa ga babban shafi
Isra'ila-Hamas

Gaza: Hamas ta amince a sake tsagaita wuta

Bangarorin Hamas da Isra’ila sun amince da sabuwar yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza ta tsawon kwanaki uku, kamar yadda bangaren Falasdianawa suka tabbatar bayan sun kammala tattaunawa a kasar Masar. Sai dai kuma zuwa yanzu babu tabbaci daga Isra’ila.

Luguden wuta da Isra'ila ke yi a Gaza
Luguden wuta da Isra'ila ke yi a Gaza REUTERS/Suhaib Salem
Talla

Amma wakilin kamfanin Dillacin labaran Faransa yace Mahukuntan Masar sun samu tabbaci daga bangarorin biyu, kuma nan bada jimawa ba ne zasu bayyana lokacin da sabuwar yarjejeniyar zata fara aiki domin tsagaita wutar zubar da jinin da ake yi a Gaza.

Kasar Masar ta bukaci bangarorin biyu su amince sabuwar yarjejeniyar ta fara aiki daga karfe 10 na dare agogon GMT.

Tuni Kakakin Kungiyar Hamas a Gaza Sami Abu zuhiri yace suna yin nazarin amincewa da sabuwar yarjejeniyar tsagaita wuta ta sa’o’I 72 domin bude kofar ci gaba da tattaunawa da Isra’ila a kasar Masar. Abu Zuhri yace suna nazarin amincewa da bukatar amma ba tare da fadin lokacin da yarjejeniyar zata fara aiki ba.

Wannan kuma na zuwa ne bayan wakilan Falasdinawa da gwamnatin Masar sun kammala zaman tattaunawa a birnin Alkahira ba tare da wakilan Isra’ila ba.

Rahotanni kuma sun ce Sojojin Isra’ila sun kashe wani yaro Bafalasdine dan shekaru 11 bayan sun bude wuta a wani sansanin ‘Yan gudun hijira a kudancin yankin yamma da kogin Jordan a yau Lahadi, Kamar yadda Jami’an kiwon lafiya suka tabbatar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.