Isa ga babban shafi
Isra'ila-Hamas

Gaza: Hamas ta ki amincewa da Isra'ila

Kasar Isra’ila ta aminta da matakin tsawaita shirin tsagaita wutar kwanaki uku da suka amince da kungiyar Hamas bayan sun kwashe kusan wata guda suna musayar wuta, amma Kungiyar Hamas ta Falasdinawa a Gaza ta ki amincewa da matakin tsawaita yarjejeniyar.

Sojojin Isra'ila suna hutawa a kusa da kan iyaka da Gaza bayan tsagaita wutar rikici ta kwanaki uku tsakaninsu da Hamas.
Sojojin Isra'ila suna hutawa a kusa da kan iyaka da Gaza bayan tsagaita wutar rikici ta kwanaki uku tsakaninsu da Hamas. REUTERS/Amir Cohen
Talla

Mataimakin shugaban Kungiyar Hamas Mussa Abu Marzuq day a halarci zaman tattauna batun tsagaita wuta a birnin Alkahira yace babu wata yarjejeniya da suka amince, kamar yadda ya rubuta a shafinsa na Twitter.

A yau Alhamis Masar zata ci gaba da jagorantar zaman sasantawa tsakanin Isra’ila da Hamas a birnin Al Kahira domin kawo karshen zubar da jini a Gaza.

Shugaban Amurka Barack Obama yace sai idan Hamas da Isra’ila sun kai zuciya nesa kafin a samu yarjejeniyar tsagaita wuta mai dorewa a Gaza.

Falasdinawa sama da 1,800 ne Isra’ila ta kashe a tsawon wata guda tana kai farmaki a Gaza, kuma yawancinsu fararen hula ne, da yara kanana kimanin 500. Sojojin Isra’ila kuma 67 ne suka mutu a rikicin.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon a karon farko ya fito karara ya soki Isra’ila kan harin da ta kai makarantun Majalisar inda mutane da dama suka mutu a Gaza.

Ban yace zargin da Isra’ila ke yi akan Hamas na ayyukan ta’adanci bai zama dalilin jefa rayukan dubban fararen hula cikin mawuyacin hali ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.