Isa ga babban shafi
Isra'ila-Hamas

Isra’ila ta janye dakarunta a Gaza

Wakilan kasar Isra’ila da kungiyar Hamas za su hau teburin tattauna yiwuwar kara wa’adin tsagaita wuta ta sa’oi 72 da suka amince bayan an kwashe makwanni ana fafatawar da ta hallaka Falasdinawa 1,870 da kuma sojin Israila 67. Tuni wakilan suka isa birnin Alkahira na Masar tare da masu shiga tsakani don halartar taron magance rikicin.

Wani Bafalasdine kwance a filin Allah da shinfidarsa bayan Isra'ila ta tarwatsa gidajen Falasdinawa a Gaza
Wani Bafalasdine kwance a filin Allah da shinfidarsa bayan Isra'ila ta tarwatsa gidajen Falasdinawa a Gaza REUTERS/Mohammed Salem
Talla

A yau Laraba yarjejeniyar sa’o’I 72 ta shiga kwana biyu. Kuma Isra’ila ta janye dakarunta daga Gaza domin mutunta yarjejeniyar tsagaita wuta da kasar Masar ta jagoranta.

Kasashen duniya suna fatar bangarorin biyu zasu cim ma yarjejeniya mai dorewa a Masar domin kawo karshen zubar da jini a Gaza

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.