Isa ga babban shafi
Birtaniya

Gaza : Wata Ministar Birtaniya ta yi murabus

Wata Ministan Birtaniya Musulma Baroness Sayeeda Warsi, ta yi murabus saboda sabanin ra’ayinta da gwamnatin kasar akan rikicin Gaza. Ministar ta mika takardar Murabus dinta ga Firaminista David Cameron tare da bayyana dalilan da suka sa ta yi murabus.

Ministan Birtaniya Musulma Baroness Sayeeda Warsi
Ministan Birtaniya Musulma Baroness Sayeeda Warsi REUTERS/Suzanne Plunkett/Files
Talla

Warsi ta soki yadda Birtaniya ke nuna goyon baya ga Isra’ila da ke kai hare hare a yankunan Falasdinawa.

Cameron yace Isra’ila tana da ‘yancin ta kare kanta daga hare haren rokoki da Hamas ke harbawa, a lokacin da ya ke mayar da martani ga Murabus din Warsi.

Maitaimakin Firaministan Birtaniya Nick Clegg yace Sayeeda Warsi ta tsaya ne akan ra’ayinta amma a fayyace komi ya ke, kuma ra’ayi ne ya banbanta game da tabargazar da ake yi a Gaza.

Clegg yace matakin Soja da Isra’ila ta dauka bai dace ba, sannan kuma abin da Hamas ke aikatawa ba a bin amincewa ba ne akan al’ummar Isra’ila.

Warsi dai ita ce Musulma ta farko da ta rike mukamin minista a Birtaniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.