Isa ga babban shafi
Afrika ta Kudu

Pistorius ya sha kuka a lokacin da ya ke ba da bahasi a kotu

Dan tseren guragun kasar Afrika ta Kudu Oscar Pistorius, ya fashe da kuka yayin da yake yiwa kotu bayanin yadda ya hallaka budurwarsa Reeva Steenkamp wacce yake zaton barawo ne ya shigo gidansa a bara.

Oscar Pistorius yana kuk a bayan da ya kammala bayar da labarin yadda ya kashe budurwarsa, Reeva Steenkamp
Oscar Pistorius yana kuk a bayan da ya kammala bayar da labarin yadda ya kashe budurwarsa, Reeva Steenkamp REUTERS/Themba Hadebe
Talla

A farkon safiyar yau talata ne Pistorius ya yiwa kotu dogon jawabi a game da soyayyarsa da Steenkamp wacce ya kashe, wacce kuma suka yi alkawarin yin aure.

A lokacin da yake bayani, yana mai zubar da haawaye da murya mai rawa daga kukan da yake yi, Pistorius ya bayyana cewa ya farka ne daga barci a cikin daren 14 ga watan Fabrairu na 2013 a firgice, bayan da ya ji karar windo da kofar ban dakinsa, wanda ya zaci barawa ne ya shigo masa gida

Inda ya ce a wannan lokaci ba abinda ya zo masa a kai illa ya nemi bindigarsa dake karkashin matashinsa a kan gadonsa domin kare kansa da budurwar tasa Reeva, wacce bayan tashinsa ba tare da juyawa ya kalli gadon ba, yake yi wa rada da ta tashi ta kira ‘yan sanda a zatonsa tana kwance ne a kan gado

A cewar Pistorius, yayin da ya ke sanda zuwa kofar ban dakin da babu wani kyaure da ya rabashi da dakin barcinsa sai yaji kamar ana shirin buda ban dakin , to a wannan lokaci ne bai ankara ba sai ya bude wuta, yana mai harbin kowane bangaren kofar.

Ya ce bayan ya dawo a dakin bacinsa ne sai bai ga budurwar tasa a gado ba, shine ya nemi taimako a ka balle kofar ban dakin.

Daga nan kuma, Pistorius ya fashe da kuka, ya kasa ci gaba da bayar da bahasin domin kuku da ya yi ta shekawa.

Bayan kammala jin wannan labari ne alkalin kotun ya sake daga zama sauraren shari’ar zuwa gobe laraba.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.