Isa ga babban shafi
Afrika ta Kudu

Pistorius ya taba yin harbi cikin fushi

A zaman sauraren karar Oscar Pistorius da aka yi a ranar Juma’a, akwai wata Tsohuwar budurwarsa da aka gabatar a matsayin shedu inda tace wata rana Dan tseren gudun na guragu ya taba harba harsashe a saman motarsa saboda ran shi ya baci a wani sabani tsakanin shi da Dan sanda.

Oscar Pistorius  a cikin zauren kotu a Pretoria ya dafe kansa
Oscar Pistorius a cikin zauren kotu a Pretoria ya dafe kansa REUTERS/Marco Longari/Pool
Talla

Tsohuwar budurwar mai suna Samantha Taylor tace Pistorius ya ci amanarta har sau biyu a soyayyarsu musamman ma daga karshe yadda ya koma yana soyayya da budurwar shi da ake tuhuma ya kashe Reeva Steenkamp.

Sai dai kuma Pistorius ya karyata labarin budurwar akan ya yi harbin bindiga cikin fushi inda tuni kuma ya ke karyata ya kashe budurwarsa da gangan.

Akwai sakon email da lauyan da ke kare Pistorius ya gabatar wanda ke cewa alakar dan wasan guragun ta kawo karshe ne da Ms Taylor a lokacin da ya fara haduwa da Reeva Steenkamp, lamarin da tsohuwar buduwar ta karyata.

Wani batu kuma shi ne yadda tsohuwar budurwar tace Pitorius ya gaya mata cewa shi a kodayaushe yana tare da bindigarsa bayan ta ga ya yi harbi a lokacin da ran shi ya baci.

Yanzu dai an dage sauraren karar zuwa ranar Litinin bayan shafe kwanaki biyar ana jin bahasi daga bakin makwabtan Pistorius wadanda dukkaninsu suka ce sun ji karar hargitsi a gidan Pistorius kafin jin karar harbin bindiga.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.