Isa ga babban shafi
Afrika ta Kudu

Pistorius ya zubar da hawaye a Kotu

A ci gaba da sauraren karar Oscer Pistorius dan tseren gudun guragu da ake tuhuma ya bindige budurwarsa a ranar masoya ta Valentine, Shedun da aka gabatar a kotun Pretoria a yau alhamis ya yi bayani ne akan yadda ya ruga zuwa gidan Pistorius domin ceton budurwar Dan wasan bayan an harbe ta da bindiga.

Oscar Pistorius a cikin zauren kotu a Pretoria
Oscar Pistorius a cikin zauren kotu a Pretoria REUTERS/Werner Beukes/Pool
Talla

A lokacin da dai shedun ke bayar da bahasi Pistorius ya dafe kansa ne tare da rufe Kunnensa.

Johan Stipp da ke bayar da shedar a gaban Alkali yace bayan harbin Reeva Steenkamp ya shiga cikin gidan Pitorius domin ceto, kuma an harbe ta ne gefen kugunta na dama yayin da jini ke kawarara daga kanta.

Anan take ne kuma shi shedun yace tun lokacin ya san cewa budurwar ba zata rayu ba, domin har sai da ya bude idonta cikin storo domin ya tabbatar da ko zata iya rayuwa don a kwashe ta zuwa Asibiti.

Tun da farko a zaman kotun, shedun da aka gabatar sun ce sun ji karar budurwar kafin jin harbin bindiga, suna masu cewa akwai karar hargitsi da hayaniya da suka ji mai nasaba da fada kafin jin harbin bindiga.

Tuni Pistorius da ake tuhuma ya bindige matarsa yak e musanta zargin yana mai ikirarin ya yi harbi ne akan tunanin wani ne ke kokarin kutsawa a cikin gidansa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.