Isa ga babban shafi
Afrika ta Kudu

Lauyoyin Pistorius sun yi watsi da shedun ‘Yan sanda

Lauyoyin da ke kare Osacar Pistorius zakaran tseren gudun nakasassu a duniya, sun yi watsi da shaidun da ‘yan sanda suka gabatar a gaban kotun da ke yi masa shari’a a jiya talata, inda hotunan ke nuna jini a cikin gidan Pistorius inda aka tsincin gawar budurwarsa Reeva Steenkamp.

Oscar Pistorius,dan tseren gudun guragu da ake tuhuma ya bindige Budurwarsa
Oscar Pistorius,dan tseren gudun guragu da ake tuhuma ya bindige Budurwarsa REUTERS/Siphiwe Sibeko
Talla

Lauyan Oscar Pistorius Barry Roux yace akwai shakka dangane da hotunan da Dan sanda mai gabatar da shaidu Bennie Van Staden ya gabatar a gaban kotun a jiya Talata, kuma wannan zai iya shafar dukkanin shaidun da ake gabatarwa kan wannan batu.

Lauyan yace daya daga cikin dalilan da suka sa shi ya ke shakku a game da hotunan da aka gabatar a gaban kutun, shi ne yadda ‘yan sanda suka kwashe kayayyakin da ke cikin dakin kafin su soma daukar hoto, kuma sakamakon yin hakan a cewar Barry, shaida na iya samun nakasu.

Har ila yau lauyan ya ci gaba da cewa, ‘yan sandarn da suka soma bincike dangane da wannnan kisa da aka yi wa Reva SteenKamp, sun taba bindigar da aka aikata kisan ba tare da sun yi amfani da safar hannu ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.