Isa ga babban shafi
Palestine

Likitoci sun ga guba a gawar Arafat na Falasdinawa

Kwararrun Likitocin Switzerland da Rasha da suka gudanar da binciken gawar Tsohon shugaban Falasdinawa Yasser Arafat sun ce akwai burbushin gubar polonium da suka gano a gawar domin tabbatar da zargin da ake yi game da musabbabin mutuwar shi.

Tsohon Shugaban Falesdinawa Yasser Arafat
Tsohon Shugaban Falesdinawa Yasser Arafat REUTERS
Talla

Binciken na Likitocin yace akwai alamun an yi amfani da guba tare da wani abu da zai iya yin kisa wajen kashe Tsohon shugaban na Falasdinawa.

A watan Nuwamban bara ne aka tono gawar Yasser Arafat domin gudanar da binciken gaskiyar musabbabin mutuwar tsohon shugaban na Falesdinawa.

Likitocin sun mika sakamakon bincikensu ne ga Uwargidan tsohon shugaban Suha Arafat da kuma wakilan gwamnatin Falesdinawa.

Rahoton na Likitocin yace duk da an kwashe tsawon shekaru 8 da mutuwar Yasser Arafat amma samfurin da suka dauka a jikinsa domin gudanar da binciken ya nuna alamar guba.

Tuni dai Uwargidan Tsohon shugaban na Falesdinawa ta bayyana imaninta da rahoton a lokacin da ta ke zantawa da kafar yada labaran Telebijin ta Al Jazeera. Suha Arafat tace mijinta ya mutu ne sakamakon cin abinci mai dauke da guba cikin makwanni hudu a shekarar 2004.

Arafat ya mutu ne a wata Asibitin Soji a kasar Faransa a ranar 11 ga watan Nuwamba. Kuma Falesdinawa suna zargin Isra’ila ce ta kashe shugabansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.