Isa ga babban shafi
Isra'ila

Binciken kashe Arafat ba damuwarmu bane, inji Isra’ila

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Isra’ila ta ce, karar da aka bude wacce wani mai shigar da karar kasar Faransa ya shigar da ke nema a fara bincike kan kisan tsohon shugaban kasar Palestine, Yasser Arafat, a shekarar 2004 ba damuwar Isra’ila ba ce.

Marigayi, tsohon shugaban Palasdinu, Yasser Arafat
Marigayi, tsohon shugaban Palasdinu, Yasser Arafat DR
Talla

A cewar mai Magana da yawun, kasar, Yigal Palmor, duk da cewa ana zargin kasar Isra’ila da kashe Arafat wannan batu bai sha mata kai ba.

Palmor ya kara da cewa, ya na fata wannan bincike zai fito da gaskiyar lamarin.

Shawarar a binciki mutuwar Arafat ta zo ne bayan iyalinsa sun shigar da kara a kasar ta Faransa a watan da ya gabata domin a tabbatar ko Arafat ya mutu ne daga guba da aka zuba masa.

Al’umar kasar Faransa dai sun nuna farin cikinsu da wannan bincike da za a fara, inda wani babban jami’in kasar, Saeb Erakat, ya fadawa Kamfanin Dillancin labaran AFP, cewa suna fatan binciken kasar ta Faransa zai gamsar da su.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.