Isa ga babban shafi
Rasha-Falesdinu-Faransa

An fara aikin tono Kabarin Arafat domin binciken abin da ya kashe shi

Falesdinawa sun fara tono kabarin Tsohon shugabansu Yasser Arafat domin Likitoci su yi binciken abinda ya kashe shi. Rahotanni sun ce an fara Janye duwatsu a Kabarin shi inda za’a kwashe kwanaki 15 ana aikin.

Marigayi, tsohon shugaban Falasdinu, Yasser Arafat
Marigayi, tsohon shugaban Falasdinu, Yasser Arafat REUTERS/Rula Halawani
Talla

Faledinawan dai suna neman  hada kai ne da Masana daga kasar Rasha da kasashen Faransa da Switzerland domin tono gawar Tsohon shugaban  don gudanar da bincike game da abin da ya yi sanadiyar ajalinsa.

A ranar 11 ga watan Nuwamban shekarar 2004 ne Arafat ya mutu a Asibitin Sojoji a birnin Paris na kasar Faransa, kuma hukumomin Faransa har yanzu ba su ce komi ba game da abinda ya kashe shi inda Falesdinawa ke zargin Isra’ila ce ta yi amfani da guba da ya kashe Shugaban.

Shugaban Falesdinawa Mahmud Abbas ya bayyana fatar ganin binciken ya tabbatar da sahihancin abinda ya kashe shi, sabanin hasashe da ake na cewar ana zaton cutar sankara da cutar kanjamau suka kashe shugaban.

Wannan ne dai karon farko da aka fadi sunan Rasha cikin kasashen da ke binciken gano abin da ya kashe Yaseer Arafat.

Dangin tsohon shugaban suna ganin ko an tono gawar shi babu wani abu da za’a gane amma suna masu ra’ayin kashe shugaban aka yi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.