Isa ga babban shafi
Rasha-Birtaniya-Syria

Kasashen duniya su rarrabu kan kai hari a Siriya

Majalisar dokokin kasar Birtaniya ta ki amincewa da niyyar da kasar ke yi na shirin kaiwa kasar Syria hari, bayan manyan kasashen duniya sun zargi gwamnatin shugaba Bashar al Assad da yin amfani da makamai masu guba akan fararen hula.‘Yan majalisun sun kwashe fiye da mintina 45 suna mahawara akan kudirin da Firaminista David Cameron ya gabatar a gaban majalisar, inda wadanda suka ki amincewa da zuwa yakin suka samu rinjaye da kuri’u 285, yayin da wadanda suka nemi a je yakin suka samu kuri’u 272.Shi kuwa Firaministan kasar Canada, Stephen Harper ya ce yana goyon bayan daukan matakin soji a kasar Syria da wasu kasashen duniya ke shirin yi, sai dai ya ce sojojin kasarsa ba za su shiga cikin dakarun da za su kai harin ba.Firaminista Harper ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da takwarorinshi na Birtaniya da Amurka da kuma Faransa a jiya Alhamis, inda yake cewa kasarsa ba ta da wani shirin fadawa cikin wani yaki a yanzu. 

Firaministan Britaniya, David Cameron lokacin da yake neman goyon bayan majalisar dokokin kasar, ta amince da kai hari a Siriya
Firaministan Britaniya, David Cameron lokacin da yake neman goyon bayan majalisar dokokin kasar, ta amince da kai hari a Siriya REUTERS/UK Parliament via Reuters TV
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.