Isa ga babban shafi
Syria-Amurka

Shugabannin Amurka da Britaniya na tattaunawa kan batun kasar Siriya

Bayan wata doguwar tattaunawa da suka yi ta wayar tarho a yammacin jiya, shugaban Amurka Barack Obama da kuma Fira minsitan Birtaniya David Cameron, sun ce shugaban kasar Syria Bashar Assad ya ki bai wa Majalisar Dinkin Duniya hadin kai, a kokarin da ake na tantance hakikannin abin da ya faru dangane da zargin yin amfani da makamai masu guba kan jama’ar kasar.A sanarwar da fadar fira ministan na Birtaniya ta fitar bayan tattaunawar, shugabannin biyu sun ce sun damu ainun a game da halin da kasar ta Syria ta fada, sannan kuma yin amfani da makamai masu guba a rikicin kasar, lamari ne da ke bukatar mayar da martani daga kasashen duniya.A dazun nan kuwa sakataren tsaron Amurka Chuck Hagel, wanda ke ziyara a birnin Kuala Lumpar na kasar Malesiya, ya ce sojan Amurka na a cikin shiri, domin kai wa Syria hari matukar dai suka sami umurnin hakan daga shugaba Obama. 

Shugaban Amurka Barack Obama tare da Firaministan Britaniya David Cameron
Shugaban Amurka Barack Obama tare da Firaministan Britaniya David Cameron
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.