Isa ga babban shafi
Syria-Amurka

Kungiyar kawayen Siriya za ta tattauna batun baiwa 'yan tawaye makamai

A ranar Asabra mai zuwa ake sa ran wasu kasashen duniya, karkashin kungiyar nan ta kawayen Siriya, za su yi taro a birnin Dohan kasar Qatar, inda za su tattauna kan bukatar tallafin da za su baiwa ‘yan tawayen kasar ta Siriya. Ministocin kasashen Faransa, Britaniya, Amurka, Jamus, Italya, Jordan, Saudi Arabiya, Hadaddiyar Daular Larabawa, Turkiyya, Masar da mai masaukin baki Qatar, duk za su halarci taron.Wani jami’in diplomasiyan kasar Faransa yace, tallafin da suke tunanin baiwa ‘yan tawayen sun hada da kayan aikin soja.Jami’in jakadancin yace, mahalartan za su duba koken da kwamandan mayakan ‘yan tawayen na Siriya ya yi, a taron da aka yi a ranar juma’a da ta gabata a birnin Ankara kasar Turkiyya, kan bukatar tallafi daga kasashen. ‘Yan tawayen sun bukaci a basu tallafin makaman kakkabo jiragen sama da na roka.A wani bangaren kuma, Shugaban kasar Lebanon Mika’el Sulaiman, yayi kira ga kungiyar Hizbullah da ta dakatar da taimakawa gwamnatin kasar Siriya a fadan da take da ‘yan tawayen kasar.Shugaban ya bayyana cewar shigar da kungiyar Hizbullah ta yi a fadan kasar Siriyan na haddasa tashin hankali a cikin kasar ta Lebanon.A wata zantawa da yayi da Jaridar As-Safir ta kasar Lebanon, Shugaba Sulaiman ya bayyana karara cewar baya tare da kungiyar Hizbullah, baya kuma goyon bayan yadda take taimakawa gwamnatin shugaba Bashar al-Assad, saboda yin hakan na kara hadasa matsala a kasar ta Lebanon. 

Wani dan tawayen kasar Siriya dauke da makami
Wani dan tawayen kasar Siriya dauke da makami REUTERS/Hamid Khatib
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.