Isa ga babban shafi
Syria

Shugaban Siriya na makokin jami'an gwamnatin shi da suka mutu

Shugaban Kasar Syria, Bashar al Assad, na zaman makokin kisan da aka yiwa wasu Manyan jami’an Gwamnatin sa jiya, yayin da kasahsen Yammacin duniya ke cigaba da kara matsa masa lamba ga Bashar al Assad ya saki madafan ikon kasar.Rahotanni sun ce akalla an hallaka mutane samada 200 a fafatawar da ake ci gaba da yi, tsakanin dakarun gwamnati da Yan Tawayen dake samun goyan bayan kasahsen duniya.Masu lura da lamura na ganin watakila karshen gwamnatin shugaba Assad ya zo.Wani jagoran ‘yan tawayen Ahmed Medani ya shaida wa Gidan Radiyon Faransa RFI, cewa mutuwar jami’an gwamnatin ta kara musu kaimi.  

Masu zanga-zangar kasar Siriya
Masu zanga-zangar kasar Siriya
Talla

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin duniya, Ban Ki Moon, da Jakadan Syria na musaman, Kofi Anan, sun bukaci kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da ya dauki matakai masu tsauri dan kawo karshen zub da jinin da ake samu a kasar.

Duk da matsin lambar da kasahsen Yammacin duniya ke yi, ana saran Rasha da China su hau kujerar naki, kan duk wani shiri na karawa Syria takunkumi.

Ban ki Moon yayi Allah wadai da harin da ya hallaka manyan jami’an Syria.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.