Isa ga babban shafi
ICC-Cote d'Ivoire

Gbagbo na Cote d'Ivoire zai sake gurfana a gaban Kotun ICC

Tsohon shugaban kasar Cote d’Ivoire, Laurent Gbagbo, zai gurfana a gaban kotun hukunta manyan laifukan yaki ta ICC da ke birnin Haque, don bai wa alkalan kotun damar yanke hukunci ko za’a iya tuhumar shi da laifin kitsa tashin hankalin da ya hallaka mutane da dama bayan zaben Shugaban kasa.

Tsohon shugaban kasar Cote d'Ivoire Laurent Gbagbo, da ke fuskantar Shari'a a kotun ICC
Tsohon shugaban kasar Cote d'Ivoire Laurent Gbagbo, da ke fuskantar Shari'a a kotun ICC REUTERS/Peter Dejong
Talla

Ana saran babban alkalin kotun, mai shari’a Silvia Fernandez de Gurmendi, ya bude zaman kotun da misalin karfe 1.30 agogon GMT.

Ana zargin akalla mutane sama da 3,000 aka kashe a rikicin siyasar kasar Cote d'Ivoire.

Gbagbo mai shekaru 67 shi ne tsohon Shugaban kasa na farko da ya gurfana a gaban kotun ICC wanda ake zargi da aikata laifukan cin zarafin al’umma da suka hada da kisa da Fyde da Dakarun da ke biyayya gare shi suka aikata bayan ya ki mika mulki ga Allasane Ouattara wanda ya kayar da shi a zaben 2010.

Masu gabatar da kara sun ce Dakarun Gbagbo sun kashe akalla mutane 706 zuwa 1,059 tare da yi wa Mata sama da 30 Fyade tsakanin watan Nuwamba na 2010 zuwa ranar 8 ga watan Mayu na 2011.

A ranar 11 ga watan Afrilu ne aka cafke Laurent Gbagbo bayan kwashe kwanaki ana yaki da dakarun shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.