Isa ga babban shafi
Syria

Gwamnatin Syria tace za ta bada goyon bayanta ga sabon mai shiga tsakani

Kasar Syria tace za ta yi aiki tare da ba da goyon baya ga sabon mai shiga tsakani rikicin kasar na Majalisar Dinkin Duniya Lakhdar Brahimi wanda ya karbi aikin daga hannun Kofi Annan tare da fatar zai fito da hanyoyin sasantawa tsakanin ‘Yan tawaye da Gwamnati.

Lakhdar Brahimi  sabon mai shiga tsakanin Rikicin kasar Syria
Lakhdar Brahimi sabon mai shiga tsakanin Rikicin kasar Syria DR
Talla

Wannan Ikirarin da kasar Syrian ta yi na zuwa ne duk da dakarun gwamnatin kasar na ci gaba da barin wuta kan ‘yan adawa a garin Aleppo, gari mafi girma na biyu a kasar.

Mukaddashin Ministan waje na kasar Syria, Faisal Mukdad ya zargi Hukumomin kasar Turkiyya wajen ba ‘Yan tawayen Syria damar amfani da kasarsu.

Kasar Turkiyya da kasar Amurka suna ci gaba da tsare-tsare domin ganin Shugaban kasar Syria Bashar Assad ya sauka lami lafiya daga madafan iko.

A cewar Mukaddashin Ministan Waje na Syrian za su bai wa sabon mai shiga tsakani Majalisar Dinkin Duniya hadin kai, kuma za su sa ido domin ganin yadda zai gudanar da ayyukan shi a kasar.

Sabon mai shiga tsakanin Lakhdar Brahimi, dan kasar Algeria ne gogagge ta fanning Diflomasiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.