Gwamnatin Ecuador za ta yi bayani akan mafakar Assange
Shugaban kasar Ecuador Rafael Correa yace a cikin wannan makon ne, ya ke sa ran nazarin bukatar wanda ya kirkiro shafin kwarmato na Wikileaks, Julian Assange ta neman mafaka a kasar bayan ya nemi mafaka a ofishin jekadancin kasar a London.
Wallafawa ranar:
Assange, mai shekaru 41 da haihuwa, ya sami mafakar siyasa a ofishin jakadancin kasar ta Ecuador da ke birnin London, tun a ranar 19 ga watan Yuni, don kaucewa mika shi kasar Sweden, inda ake zargin shi da laifin yin fyade.
Assange yace yana fargabar idan aka mika shi Sweden, daga can kuma za a iya mika shi Amurka, don a tuhumar shi da laifin leken asiri.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu