Isa ga babban shafi
Chile

Yau za’a fara ceto mahakan kasar Chile 33

YAU ne ake saran fara zakullo mahakar kasar Chile 33, dake karkashin kasa sama da watanni biyu. Tuni dai kafofin yada labaran duniya, sama da 1,000 suka girke kayan aikinsu, a bakin ramin, dan shaidawa duniya yadda aikin zai kaya, yayin da Yan’uwa da abokan arzikin mahakan suka mamye bakin ramin.Shugaban kasar Chile, Sebastine Pinera, na daga cikin wadanda zasu kasance a bakin ramin, yayin da za’a fara gudanar da aikin.Ministan ma’adinan Chile, Laurence Golborne, ya bayyana gamsuwa da aikin ceton, kuma yace za’a fara zirara jami’an agaji, da na lafiya, dan taimakawa mahakan, kafin fara janyo su.Baban jami’in dake kula da aikin, Injiniya Andre Sougarret, yace an jarraba aikin ceton, kuma an gamsu da yadda ya kaya. 

kasar Chile
kasar Chile Reuters /Mariana Bazo
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.