Isa ga babban shafi
Chile

An gano mahakan Chile da ransu bayan kwashe kwanaki 17 a birne

SHUGABAN kasar Chile, ya tabbatar da cewar, wasu mahaka 33 da kasa ya birne na kwanaki 17, suna nan da ransu.Shugaban kasar, Sebastian Pinera ya sanar da haka, bayan mahakan sun turo wasika ta wani rami, inda suke cewa dukkansu suna cikin koshin lafiya.Shugaban kasar yace, ya ga hotunan mahakan da aka dauka ta kafar talabijin, suna nan da ransu, kuma zai dauki watanni kafin a ciro su daga ramin, mai zurfin sama da kafa 2,000.Kafin dai jiya, ba wanda yaji duriyar mahakan, abinda ya sa yan’uwa da abokan arziki suka dauka sun mutu.Bayan samun bayanai, daga masu aikin agaji, shugaban kasar Sebastian Pinera, da kansa yaje mahakar, inda ya yiwa manema labarai bayani. 

Shugaban Chile Sebastian Pinera
Shugaban Chile Sebastian Pinera AFP/ HECTOR RETAMAL
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.