Isa ga babban shafi
Chile

An cim ma gagarimar nasara a kokarin zabaro ma'aikatan kuza

Yau Asabar Injiniyoyi suka cim ma nasarar isa ga ma’aikatan nan na kuza da wata ruftawa ta binne su a karkashin kasa tsawon fiye da watanni biyu, inda suka kammala bututu ko kuma kurar-zabari da za a yi amfani da ita wajen zakulo su, nan da wasu ‘yan kwanaki.Injiniyoyin da suka tona ramin sun yi isharar nasarar da suka samu ne ta hanyar yin wata busa, kana suka rika tsalle suna rungumar junansu a yanayin farin ciki, kuma daga bisani daruruwan ‘yan uwan ma’aikatan kuzan da suka tare a kusa da wurin, suka shiga cikin wannan sowa.Da sanyin safiyar Talata mai zuwa ake sa ran fara yin zabarin mutanen ta cikin wani katon guga da aka kera zuwa zurfin mita 622; wato kafa dubu biyu da arba’in, amma fa sai an tantance yiwuwar hakan.  

C.Magnard/RFI
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.