Isa ga babban shafi
Syria

Mayakan IS sun kwace ikon Palmyra na Syria

Mayakan IS sun kwace ikon garin Palmyra mai dimbin tarihi a Syria, masu sa ido a rikicin kasar sun ce mayakan sun kwace ikon garin baki daya bayan dakarun gwamnati sun fice daga yankin. Wannan babbar nasara ce ga IS bayan kungiyar ta kwace Ramadi a Iraqi.

Garin Palmyra mai dinbim tarihi a Syria
Garin Palmyra mai dinbim tarihi a Syria Unesco/G. Degeorges
Talla

Tun a jiya Laraba Mayakan suka fara rusa garin mai cike da kayan Tarihi.

Hukumar Majalisar Dinkin Duniya da ke kula da ci gaban al’adu da Ilimi da kimiya ta UNESCO ta bayyana takaicinta akan yadda ake rusa kayayyakin tarihin kasashen Larabawa a Syria da Iraqi.

Kwace ikon Palmyra na zuwa ne bayan mayakan sun yi nasarar kwace ikon garin Ramadi da ke kusa da Badagaza babban birnin kasar Iraqi.

Tuni kuma Mayakan IS suka tarwatsa biranen Nimrud da Mosul masu dimbin tarihi a Iraqi.

Daruruwan mutane ne suka fice yankunan da Mayakan IS suka kwace wadanda ke gwagwarmayar kafa daular musulunci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.