Isa ga babban shafi
Yemen-Saudiya

Saudiya na ci gaba da jagorantar hari a Yemen

Jiragen yakin Saudiya da na kawayenta sun ci gaba da yi wa ‘Yan tawayen Yemen luguden wuta a Sanaa a yau Talata bayan wa’adin yarjejeniyar tsagaita wuta ta kwanaki biyar ya cika a jiya Litinin. Yanzu haka bangarorin siyasar kasar sun bayyana nuna goyon bayansu ga hare haren sama da ake kai wa ‘Yan tawayen Huthi mabiya Shi’a.

Tun a Watan Maris Saudiya ta kaddamar da hare hare akan Yan tawayen Yemen
Tun a Watan Maris Saudiya ta kaddamar da hare hare akan Yan tawayen Yemen REUTERS/Mohamed al-Sayaghi
Talla

Tun a jiya Litinin ne jiragen yakin Saudiya da na kawayenta suka ci gaba da yi wa ‘Yan tawayen Huthi mabiya shi’a luguden wuta a a biranen Sanaa da Aden bayan Saudiya ta zargi ‘yan tawayen da karya yarjejeniyar tagaita wuta ta kwanaki biyar da suka amince domin shigar da kayan jinkai.

Yanzu haka kuma bangarorin siyasar kasar sun bayyana nuna goyon bayansu ga hare haren da Saudiya ke jagoranta akan ‘yan tawaye domin ba gwamnatin Abedrabbo Mansour Hadi komawa kan aikinta na jagorantar kasar.

Shugaban na Yemen wanda ya tsere zuwa Saudiya ya shaidawa mahalarta taron rikicin Yemen da aka gudanar a birnin Riyadh cewa suna goyon bayan hare haren da Saudiya ke kai wa ‘Yan tawaye.

A makon gobe ne Majalisar Dinkin Duniya za ta jagoranci taron sasanta rikicin kasar ta Yemen, yayin da aka bayyana cewa adadin mutane 1850 aka kashe, tare da sa mutane 500,000 kauracewa gidajensu tun barkewar rikicin kasar a watan Maris.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.