Isa ga babban shafi
Yemen-Saudiya

Saudiyya ta dawo da luguden wuta a Yemen

kasar saudiyya ta kaddamar da sabon hare-hare akan 'yan tawayen Huthi da ke kasar Yemen, adai-dai wannan lokaci da wa’adin tsagaita bude wuta ta kwanaki biyar ke cika.Tun kafin wayewar gari yau littini ne dai wa'adin tsagaita bude wutan ya kare, duk da cewa kungiyoyin bada agaji na cewa a kara wa'adin tsagaita wutan.

tashin bama-bamai a yemen
tashin bama-bamai a yemen REUTERS/Stringer TPX IMAGES OF THE DAY
Talla

Majiyoyi na cewa da cikan wa'adin, jiragen yakin kasar Saudiyya da abokanta suka fara luguden wuta ta sama, musamman a makwancin ‘yan tawaye da ke fadar Shugaban kasa da suka kwace, a birnin Aden , da dai wasu sansanonin ‘yan tawayen da ke kasar.

Ganau sun ce an kai wasu hare-haren garuruwan Tawahi da Khor Maksar, da kodashike, babu bayanai akan irin hasarar da aka tafka ya zuwa yanzu.

Sabbin hare-haren na zuwa ne duk da cewa bayaga kungiyoyin bada agaji ,shima jakadan MDD da ke Yemen Ismail Ould Sheikh Ahmad ya nemi ala tilas a kara wa'adin tsagaita wutan.

Wani jami'in kiwon lafiya a birnin Aden ya ce fararen hula akalla 517 ne suka gamu da ajalinsu sakamakon barin wuta da akayi a birnin Aden cikin kwanaki 50 da suka gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.