Yemen za ta janye jami'an diflomasiyya daga kasar Iran
Gwamnatin kasar Yemen da ke gudun hijira ta bayyana aniyar janye jami’an jakadancinta daga Iran, saboda abinda ta bayyana a matsayin shishshigin da hukumomin birnin Tehran ke yi a harkokin kasar.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Wata sanarwar da fadar shugaba Abedrabbo Mansour Hadi ta fitar, ta zargin Iran da marawa mayakan Huthi baya, a yakin da suke yi da gwamnatin kasar ta Yemen mai samun goyon bayan kasashen Larawaba.
A karshen watan Maris Shugaba Hadi ya tsere zuwa birnin Riyadh na kasar Saudiyya lokacin da mayakan na Huthi suka nufi inda ya fake a birnin in Aden.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu