Isa ga babban shafi
Yemen

An fara raba kayan jin kai ga mutanen Yemen

Kungiyoyin agajin kasashen duniya sun fara rarraba kayan tallafi ga fararen hula a kasar Yemen da suke matukar bukata. Wannan na zuwa a daidai lokacin da kwamitin hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ke cewa al’ummar kasar sun fada cikin bala’i.

Mutanen Yemen da ke cikin mawuyacin hali
Mutanen Yemen da ke cikin mawuyacin hali REUTERS/Mohamed al-Sayaghi
Talla

An samu shigar da kayar ne bayan yarjejeniyar tsagaita wuta ta fara aiki, inda da aka shafe makwanni bakwai, kasar Saudiya da kawayenta na kasashen Larabawa luguden wuta kan Mayakan Huthi ‘yan Shi’a.

Rahotanni daga Yemen sun ce an samu lafawar rikicin kasar a karon farko tun lokacin da Saudiya da kawayenta suka kaddamar da hare haren jiragen sama kan mayakan Huthi ‘Yan shi’a a ranar 26 ga watan Maris, bayan amincewa da matakin tsagaita wuta domin shigar da kayan jin kai ga mutanen kasar.

Ko da ya ke Saudiya ta yi zargin cewa ‘Yan tawaye sun karya yarjejeniyar bayan sun harba makamin roka a Jazan da Najran da ke kan iyaka tsakanin Saudiya da Yemen.

Saudiya tare da tallafin Amurka, na bayar da taimako ne ga shugaba Abedrabbo Mansour Hadi, da ya tsere daga kasar Yemen, bayan mayakan Huthi sun karbe fadar shi da ke birnin Sanaa.

Bangarorin da ke rikici a Yemen sun amince a tsagaita wuta na tsawon kwanaki biyar domin shigar da kayan jin kai ga mutanen Yemen.

An shafe watanni ana gwabza fada tsakanin ‘Yan tawayen Huthi mabiya Shi’a da ke samun goyon bayan Iran da kuma dakarun da ke biyayya ga shugaban kasa Abedrabbo Mansur Hadi da Saudiya ke marawa baya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.