‘Yan tawayen Syria sun karbe Jisr al Shughur
‘Yan tawayen Syria sun karbe ikon garin Jisr Al-Shughur, gari na karshe da ke hannun ikon gwamnatin kasar a lardin Idlib. Rahotanni sun ce dakarun Gwamnati sun yanka fursunoni 23 da suka kame kafin su fita garin na Jisr.
Wallafawa ranar:
Tun a ranar Alhamis ne ‘yan tawayen na Syria tare da taimakon mayakan Al Qaeda suka kaddamar da farmaki a yankin, kuma rahotanni sun ce har zuwa yau Assabar suna ci gaba da gwabza fada da dakarun gwamnatin Syria.
Masu sa ido a rikicin kasar sun ce dakarun shugaba Bashar Assad sun fice daga yankin bayan ‘Yan tawaye sun fatattake su.
Rahotanni sun ce akalla mutane 10 aka kashe a musayar wutar da aka yi tsakanin ‘Yan tawaye da dakarun gwamnati.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu