Isa ga babban shafi
Syria

Mutane 220,000 suka mutu a Syria

Kungiyar da ke sa ido a rikicin Syria tace sama da mutune 220,000 aka kashe a rikicin Syria da aka shafe shekaru hudu ana zubar da jini tsakanin dakarun gwamnatin shugaba Bashar al Assad da ‘Yan tawayen da ke adawa da shi.

Yankin Qastal Harami a syria  inda Dakarun Bashar Assad suka kai hare haren bama bamai
Yankin Qastal Harami a syria inda Dakarun Bashar Assad suka kai hare haren bama bamai REUTERS
Talla

Rahaton na kungiyar, ya bayyana cewa adadin mutane 222,271 suka mutu tun soma rikicin a watan Maris din 2011.

Rahoton ya ce mutane 67,000 da aka kashe fararen hula ne kuma daga cikinsu 11,000 yara kanana ne.

Rahoton ya ce kimanin dakarun gwamnati 47,000 aka kashe a rikicin, daga cikinsu kuma akwai 3,000 ‘yan kasashen waje da ke taimakawa Bashar Assad.

Akalla ‘yan tawaye 40,000 aka kashe a cewar rahoton, kuma akwai mayakan da ke taimaka ma su na kasashen waje irin su al Nusra 28,000 da aka kashe a rikicin.

Kungiyar tace adadin na iya zarce alkalumman da ta fitar domin akwai mutanen Syria da dama da suka bace.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.