Isa ga babban shafi
Iraq

Moqtada Sadr ya bukaci Al-Maliki ya gaggauta yin marabus

A daidai lokacin da mayakan jihadi ke ci gaba da gwabza fada da dakarun gwamnatin kasar Iraki, shi kuwa Firai ministan kasar Nouri Al-Maliki na ci gaba da shan suka ne daga abokannin hamayyarsa na siyasa.

Moqtada Sadr, jagoran mayakan sa-aki 'yan Shi'a a Iraki
Moqtada Sadr, jagoran mayakan sa-aki 'yan Shi'a a Iraki
Talla

Jagoran mayakan sa-kai na mabiya mazhabar Shi’a a kasar Sheikh Moqtada Sadr, na daga cikin wadanda suka soma yin kira ga Al-maliki da ya gaggauta sauka daga kan mukaninsa.

Sadr ya yi zargin cewa Firai ministan ne ya haddasa barkewar yakin basasa a Iraki, ta hanyar kirkiro da sabani da gangan tsakanin manyan ‘yan siyasar kasar mabiyar Sunni da kuma ‘yan Shi’a, lamarin da ke ci gaba da jefa sha’anin tsaron kasar a cikin hali na rashin tabbas a cewar Moqtada Sadr.

Maliki dai ya dare kan wannan mukami ne tun shekara ta 2006, kuma yanzu haka yana fatar Majalisar Dokokin kasar za ta sake zaben sa domin ci gaba da rike matsayinsa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.