Isa ga babban shafi
Iraqi-Indiya

Ma'aikatan Jinya Indiya da yakin Iraqi ya rutsa da su zasu koma gida

Yau ake sa rai tawaggar ma’aikatan Jinyar nan ‘yan kasar India su 46, da yakin da ake yi a kasar Iraqi ya rutsa da su, za su koma gida. An sako sune daga birnin Mosul, inda ake tsare da su, bayan da ‘yan tawayen kasar suka karbe Birnin Tikrit, inda suke aiki a wani asibitin kafin ‘yan tawayen su fara kai hare hare ba kakkautawa a yankin.Ma’aikatan Nurse Nurse din sun shiga wani jiragin saman da aka yi hayar shi, daga Birnin Arbil na kasar ta Iraqi, inda zai isa garin sun a Kerala a India da misalin karfe 12 na ranar yau Asabar, bayan ya tsaya a Birnin Mumbai. 

wasu ma'akatan jinya suna gudanar da aikin su
wasu ma'akatan jinya suna gudanar da aikin su REUTERS/Stringe
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.